Teriyaki rice

Teriyaki rice tana da dadi sosai duk Wanda yaci saida ya yaba jinjina ga cookpad admins dasuka koya mana wannan girki mai dadi. Ana saka sausage na musanya da hanta saboda bama sonshi nida maigidana

Umarnin dafa abinci
- 1
A wanke shinkafa sai a tafasa ya kusa dahuwa, sai a juye a abin tacewa ruwan ya tsan tsane
- 2
Sai a zuba mai a tukunya ya danyi zafi, sai a zuba yankakkiyar albasa in tayi laushi a cikin mai, sai a zuba yankakken karas da koren wake a jujjuya, sai a zuba hanta ko sausage, sai a zuba mai dandano da sauran kayan kamshi
- 3
Sai a kawo shinkafar da aka tafasa a zuba a jujjuya, sai a zuba teriyaki source akara juyawa, sai a rufe a rage wuta ya turara. Sai aci da hadin salad mai dadi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai