Miyar egusi

B.Y Testynhealthy @B66579858
Wannan miyace mai dadi da ake cinta da tuwon ko sakwara da sauransu
Miyar egusi
Wannan miyace mai dadi da ake cinta da tuwon ko sakwara da sauransu
Umarnin dafa abinci
- 1
A wanke nama da ganda a tafasa tare da albasa da maggi 2 da kayan kamshin girki
- 2
A jajjaga attaruhu da tattasai da tafarnuwa da albasa, a soya da manja sama sama
- 3
Sai a hada soyayyen tattasai da attaruhu da albasa tareda tafasasshen nama da ruwan nama a dora ya tafasa
- 4
Sai a yanka albasa a jajjagata, sai a zuba egusi a cikin albasa a kara jajjagawa tare
- 5
Sai a saka maggi da zuba egusi a ruwan miyan a barshi ya dahu
- 6
A yanka alayyahu ko ugu a wanke a tsane, sai a zuba a miyar, a bashi mintuna 5-7. Aci da tuwo ko egusi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10985600



sharhai