Danderu

Hanyar dahuwar nama ne ta gargajiya wanda kaka ta take yi duk lokacin babbar sallah nima na taso Inason shi sosai dan haka nake yi wasu lokacin
Danderu
Hanyar dahuwar nama ne ta gargajiya wanda kaka ta take yi duk lokacin babbar sallah nima na taso Inason shi sosai dan haka nake yi wasu lokacin
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke naman ki tas ki sassaga jikin da wuka,
- 2
Sai ki jajjaga attarugu, Albasa, tafarnuwa da citta kihadasu da curry, gishiri, maggi, garin mosoro da mai ki kwaba
- 3
Sai ki shafa a jikin naman duk jiki lungu lungu kota ina hadin yashiga jiki sosai
- 4
Sai kiyi wrapping da foil pepper
- 5
Sai kidaura tukunya akan wuta kizuba ruwa sai kisa tray silver ko murfin tukunya acikin tukunyar kar ruwan yawuce murfin tukunyar sai kidauko naman kidora akan tray ko murfin tukunya sai kirufe tukunya da buhu kafin ki daura murfin tukunya
- 6
Sai kibarshi ya nuna a hankali, nidai kwana yakeyi akan wuta amma akan garwashi ya nuna a hankali.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (2)