Dambun Masara

Wannan girki yanada dadi sosai kuma yana kara lafiya saboda sinadaran da aka hada a cikin girkin suna kara lafiya #kadunastate2807
Dambun Masara
Wannan girki yanada dadi sosai kuma yana kara lafiya saboda sinadaran da aka hada a cikin girkin suna kara lafiya #kadunastate2807
Umarnin dafa abinci
- 1
A Dora ruwa kadan a tukunya sai a dora madambaci akan tukunyar sai a yanki dan karamin buhu a wanke a shimfida a cikin madambaci, wanke tsakin masara a zuba akan buhun, sai akara rufa wani buhun karami sannan akara rufewa da murfin ya turara kamar na minti 20
- 2
In yadan fara laushi sai a sauke a juye a baho, a dauraye zogale a zuba, a dan daka gyada sama sama a zuba, a zuba jajjagaggen attaruhu da yankakkiyar albasa, a murmusa maggi, a zuba mai a juya sosai
- 3
A kara dora tukunya da ruwa a ciki kadan a mayarda madambaci da buhun, sai a zuba hadi dambun akan buhu a rufewa da wani karamin buhu sai a kara rufewa da murfin tukunya a bashi yayi mintuna 20-30, in yayi laushi sai a sauke. Aci da zafinsa
Keywords
Similar Recipes
More Recipes



sharhai