Miyar karasu

KADIS KITCHEN
KADIS KITCHEN @cook_17737060
KANO STATE

ZAA iya cin wannan miya da tuwo waina ko.sinasir fanke da sauransu

Miyar karasu

ZAA iya cin wannan miya da tuwo waina ko.sinasir fanke da sauransu

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Kayan miya
  2. Nama
  3. Alayyahu+yakuwa
  4. Gyadar kunu(markadaddiya)
  5. Albasa ki raba gida 2 rabi kiyayyanka da girma rabin kuma kanana
  6. .thyme,magi,gishiri
  7. daddawa yar kadan. Cray fish
  8. mai da manja
  9. Romo
  10. tafarnuwa

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki tafasa namanki da kayan kanshi sai ki ajje
    agefe sai ki dakko alayyahunki da yakuwa ki wanke sai ki
    hadesu ki tafasa yana tafasa sai ki kawo turmi sai ki daka
    wannan alayyahu din da yakuwa sai ki ajje agefe

  2. 2

    Sai ki dora
    tukunyarki sai kisa manja da mai kadan sai kawo albasarki
    me kana nan yanka sai ki kawo tafashashn namanki sai ki
    saka sai ki motsa ki bari yadan soyu sai ki kawo tafarnuwa
    kisa kikawo citta kisa sai ki motsa tadanyi 2mnt sai ki kawo
    kayan miyar ki sai ki saka ki saka daddawa kadan ki saka
    thyme sai spices ki motsa ki barta ta soyu.

  3. 3

    Sai ki samo wata robar ki dibi wannan gyadar sai ki saka ki
    kawo ruwa ki dan damata sai ki aje a gefe.
    sai ki koma gun miyarki in ta soyu sai ki bude ki saka kayan
    dandano da gishiri da romo da cray fish da curry sai ki
    motsa sai ki kawo gyadar nana taki ki zuba amma baa gu
    daya ba zagayawa da kwanon zaki nayi harki juye duka
    amma karki motsa sai ki rage wuta sai ki rufe tayi kmr
    3-5mnt

  4. 4

    Shikenan sai ki bude ki saka manyan albasarki sai
    ki motsa ki sa ka ganyenki ki motsa tayi kamr 3mnt
    shikenan sai ki sauke.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
KADIS KITCHEN
KADIS KITCHEN @cook_17737060
on
KANO STATE

Comments

Similar Recipes