Hoce Dan Mafara

Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
Sokoto

#repurstate
Hoce kenan, Dan Mafara ya na da dadi sosai😋 kuma ana sarrafashi salo daban-daban, kamar yin Shi da miyar ganye, miyar kuka, ko a hada da kuli-kuli a yi datu😋 kamar dai yanda na yi. Wasu ma suna hada Shi da lemun kwalba kamar yanda ake yi da bredi🥰

Hoce Dan Mafara

#repurstate
Hoce kenan, Dan Mafara ya na da dadi sosai😋 kuma ana sarrafashi salo daban-daban, kamar yin Shi da miyar ganye, miyar kuka, ko a hada da kuli-kuli a yi datu😋 kamar dai yanda na yi. Wasu ma suna hada Shi da lemun kwalba kamar yanda ake yi da bredi🥰

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

15 minti
mutum 2 yawan a
  1. 1Hoce
  2. Garin kuli-kuli Kofi daya
  3. Ganyen latas daidai bukata
  4. Albasa in ana so
  5. Man kuli
  6. Ruwa rabin kofi
  7. Jan tattasai
  8. Attarugu
  9. Tafarnuwa

Umarnin dafa abinci

15 minti
  1. 1

    Za mu dauko hoce my marmasa Shi yanda ze yi dadin motsawa

  2. 2

    Mu gyara ganyen latas mu wanke kamar haka

  3. 3

    Se mu hada garin kuli-kuli da attarugu da tafarnuwa a cikin turmi

  4. 4

    Za mu samu roba ko wuri me kyau mu hada garin kuli-kuli da ruwa kwabin ya yi kauri kadan

  5. 5

    Zamu hada marmasashshen hoce, ganyen latas da albasa wuri data mu hada mu motsa kamar dai yanda ake ko wane datu.

  6. 6

    Sai a samu mazubi me kyau a zuba se ci...Amma a ajiye ruwa a kusa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
rannar
Sokoto

Similar Recipes