Salad din dankali da kifi

Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
Sokoto

#ramadansadaka
Wannan girki ya na da dadi sosai musamman lokacin buda baki.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

hr 1mintuna
2 yawan abinchi
  1. Kifi
  2. Dankali
  3. Mai
  4. Tarugu
  5. Albasa
  6. Dandano da gishiri
  7. Kayan kamshi
  8. Kabeji
  9. Koren tattasai

Umarnin dafa abinci

hr 1mintuna
  1. 1

    A wanke kifi a yanka, a kuma tsane Shi a kwando ko waya kamar haka

  2. 2

    A share kifi da kayan kamshi da dandano

  3. 3

    A Jira kamar minti 20 se a soya

  4. 4

    A sa tissue paper a tsane Mai

  5. 5

    A fere dankali a wanke, sannan a sa gishiri kadan, a soya a tsane a kwando

  6. 6

    A dauko tukunya a sa kan wuta a zuba Mai kadan da albasa a soya kadan

  7. 7

    A zuba tarugu da Korean tattasai a soya Sama sama

  8. 8

    A zuba ruwa kadan tare da kayan kamshi da dandano a motsa

  9. 9

    Se a zuba soyayyen dankali da yankakken kabeji a motsa

  10. 10

    Se a sa soyayyen kifi a sake motsawa su hade jikinsu

  11. 11

    Se a rufe a sa wuta kadan minti biyu a sauke

  12. 12

    Za a iya ci da shinkafa ko taliya ko ma hakanan kawai😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
rannar
Sokoto

Similar Recipes