Lemon abarba da beetroot

Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617

Wannan lemo ne mai dadi da amfani a jiki, ina yawan yiwa iyalina wadannan nau'in lemuka saboda kara lafiya da kariya daga shan lemuka masu illah a jikin dan Adam.

Lemon abarba da beetroot

Wannan lemo ne mai dadi da amfani a jiki, ina yawan yiwa iyalina wadannan nau'in lemuka saboda kara lafiya da kariya daga shan lemuka masu illah a jikin dan Adam.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti goma
mutane 4 yawan abinchi
  1. Abarba babba guda daya
  2. beetroot manya guda biyu
  3. Danyar citta manya guda biyu
  4. Ruwan sikari

Umarnin dafa abinci

minti goma
  1. 1

    A samu abarba a bare bawonta a Wanketa sai a yanka kanana a ajiyeta a gefe.

  2. 2

    Shima beetroot za'a fere bawonsa a wanke ayanka kanana a ajiye a gefe

  3. 3

    A samu itama danyar citta a bare bawonta a wanke a yanka kanana.

  4. 4

    A samu na'urar markade a zuba duka kayayyakin a markada. Asamu rariya a tace ruwan. Sai a zuba ruwan dafaffen sikari azuba yandda dandanon zaiyi daidai a baki. A zuba a mazubi mai tsafta.

  5. 5

    Asakashi a na'urar sanyi yayi sanyi ko a saka kankara. A sha lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617
rannar

Similar Recipes