Tura

Kayan aiki

  1. Dankalin turawo
  2. Koran tattasai
  3. Karas
  4. Mayonnaise
  5. Kwai
  6. Sugar
  7. Parsley
  8. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko xaki fara fereyi dankalin turawarki kiyi masa madaidaicin yanka yadda xaiyi saukin shiga bakinki idan kintashi ci saiki tafashi bayan ya dahu saiki tace shi kitsane a abun tsane taliya

  2. 2

    Saiki dauko karas dinki ki fereye bayan saiki gogashi shima ki ajeye agefe
    Saiki dauko koran tattasaiki kiyanka shi kicire yayan cikin shima kiyanka kamar yankan da kk yiwa dankalin turawarki saiki dauko ganyen parsley

  3. 3

    Dinki ki yanyanka kanana sosai shima ki ajeshi a gefe saiki dauko wani maxubin daba ki xuba sugar daidai yadda kk so sannan kikawo bama itama ki xuba kikawo gishiri kadan bada yawaba kixuba saiki dauko wannan parsley din kixuba

  4. 4

    Saiki jujjuya sosai harsaiya hade sosai saiki saka a firji sannan saiki dauko dankalin turawarki da koran tattasaiki da karas dinki da dafaffen kwanki bayan shima kinmai irin yankan da kk yiwa dankalin turawarki da koran tattasaiki saiki samu

  5. 5

    Maxubi mai kyau kixuba su duka saiki juya sannan ki dauko wannan hadin na bama da sugar kixuba ki jujjuya sosai saiki saka a firji idan yy dan sanyi yafi dadi sosai

  6. 6

    Shikenan sai ci Amman fa akwai dadi ma tuka gaya ba'a bawa yaro mai kiwa 😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Zee's cake and more
rannar

sharhai (2)

Similar Recipes