Miyar kabeji

Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
Sokoto

Kabeji na da amfani kwarai da gaske kuma ya na da hanyoyin sarrafawa da dama, wannan miya za ta tafi da farar shinkafa, taliya, dafa Duka da sauransu😋

Miyar kabeji

Kabeji na da amfani kwarai da gaske kuma ya na da hanyoyin sarrafawa da dama, wannan miya za ta tafi da farar shinkafa, taliya, dafa Duka da sauransu😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 20mintuna
2 yawan abinchi
  1. Kabeji
  2. Naman kaza
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Tattasai
  6. Mai
  7. Dandano
  8. Kayan kamshi

Umarnin dafa abinci

minti 20mintuna
  1. 1

    Za a tafasa kaza da dandano da kuma kayan kamshi, har ta yi laushi

  2. 2

    Za a yanka kabeji yanda ake bukata, a wanke a tsane ruwa

  3. 3

    Za a Dora tukunya a wuta da Mai da albasa a ciki, a soya jajjagen tarugu da tattasai

  4. 4

    Bayan sun soyu kadan za a zuba Naman kaza bayan an cire Kashi an yanka kanana

  5. 5

    Za a Kara kayan dandano da kuma kayan kamshi da ruwa kadan, se a rufe

  6. 6

    Idan ruwan ya tsane, se a zuba yankakken kabeji a motsa a rufe na minti daya

  7. 7

    Bayan minti daya miya ta kammala se a ci da abunda ake so😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryam's Cuisine
Maryam's Cuisine @cook_19163402
rannar
Sokoto

sharhai (3)

Similar Recipes