Macaroni da miyan kayan lambu

Safeeyyerh Nerseer
Safeeyyerh Nerseer @3252a

Inason kayan lambu, sunada anfani ajiki shiyasa nayi wannan miyar

Macaroni da miyan kayan lambu

Inason kayan lambu, sunada anfani ajiki shiyasa nayi wannan miyar

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Macaroni
  2. Kabeji
  3. Caras
  4. Green beans
  5. Maggi
  6. Gishiri
  7. Mangyada
  8. Kayan kanshi
  9. Nama
  10. Kwai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki dafa macaroninki da kwanki ki tsane kisa agefek

  2. 2

    Seki wanke green beans, da caras sai ki yayyankasu madaidaita, saiki dorasu awuta su dahu sannan saiki ajiye agefe seki yanka kabejinki ki wanke shi shima ki ajiye agefe

  3. 3

    Seki wanke namanki ki tafasashi da kayan kanshi da maggi da gishi inso samune kiyankasu kanana yadda zaifi dadin ci

  4. 4

    Sekisa tukunya awuta kizuba mangyada Dan daidai inya soyu seki dauko namanki dakika tafasa seki soyashi acikin man inya soyu seki zuba caras, green beans da kabejinki seki zuba maggi da gishiri sai kidansa ruwa kadan sabida Maggi yashiga kayan lambunki kuma kabejin yadahu

  5. 5

    Inkinga yayi seki sauke. Zaki iyaci da taliyama ba lallai sai macaroni kadai ba

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Safeeyyerh Nerseer
rannar
My love for cooking is as far as I like something I would enter kitchen and prepare it that gives me joy.
Kara karantawa

Similar Recipes