Tsire

Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
Kano

#Namansallah# inason tsire a rayuwa ta shiyasa na yanke shawarar gwada basira ta nayi a gida kuma alhmdllh tsiren nan yayi dadi sosai dan munji dadin shi sosai nida iyalina.

Tsire

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

#Namansallah# inason tsire a rayuwa ta shiyasa na yanke shawarar gwada basira ta nayi a gida kuma alhmdllh tsiren nan yayi dadi sosai dan munji dadin shi sosai nida iyalina.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Nama kilo d'aya
  2. Garin kuli-kuli kofi d'aya da rabi
  3. Mai cokali biyu
  4. Maggi guda biyu
  5. Gishiri rabin cokalin shayi
  6. Yajin barkono cokali d'aya
  7. Kayan k'amshi cokalin shayi
  8. Kabeji kwatan karami
  9. Tumatir madaidaita guda biyar
  10. Albasa rabin karama
  11. Cocumber madaidaici
  12. Tsinken tsire

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Kayan da nayi amfani dasu kayan k'amshi na dakakkiyar citta ce da masoro da kanin fari da tafarnuwa.

  2. 2

    Da farko na wanke hannuna tatas sannan na wanke namana sosai, saina dinga d'auka da d'ad'd'aya ina yankashi da wuk'a a kwance saboda yayi fad'i harna gama.

  3. 3

    Saina d'auko tsinke na ina zurawa da d'ad'd'aya harna gama jerawa a jikin tsinken tsire saina ajiye shi a gefe.

  4. 4

    Saina samu turmi na saka gishiri maggi da yajin barkono da kayan k'amshi na daka saina juye garin k'uli-k'uli na k'ara lillisawa saina juye a faranti.

  5. 5

    Saina dinga d'aukar naman dana saka jikin tsinke ina sakashi cikin k'uli-k'uli ina dandannawa dan k'ulin ya kama jikin naman harna gama.

  6. 6

    Saina d'auko wayar gasa nama na jajjera tsiren akai na saka a oven.

  7. 7

    Da naman yayi kamar minti 15 yana gasuwa saina bude oven d'in na fito dashi na juya na d'an yaryad'a mai na maidashi cikin oven.

  8. 8

    Har zuwa ya k'ara minti 10 saina kashe oven d'in na fito da tsiren.

  9. 9

    Saina koma na yanka kabeji kanana na saka ruwa na wanke shi da gishiri sannan na wanke tumatir da albasa da cocumber.

  10. 10

    Sannan saina yanka tumatir da albasa da cocumber.

  11. 11

    Daga haka na cire tsiren daga jikin tsinke na saka a faranti nayi mishi ado da kabeji da tumatir da albasa da cocumber nad'an saka yaji a gefe.

  12. 12

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes