Dambun nama

Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
Jigawa State Nigeria

Dambun nama hanya ce ta sarrafa nama yadda bazai lalace ba sannan yanada dadi wajen ci #namansallah

Dambun nama

Dambun nama hanya ce ta sarrafa nama yadda bazai lalace ba sannan yanada dadi wajen ci #namansallah

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutum 6 yawan
  1. Nama maras kitse da jijiya yawan naman kamar cinyar saniya daya
  2. Curry roba daya (ducros)
  3. Thyme cokali daya babba
  4. 40Maggi guda
  5. 5Albasa manya guda
  6. 2 Tafarnuwaqwallo
  7. cokaliKanimfari rabin qaramin
  8. Taruhu daidai buqata
  9. Mai (na gyada ko na kanti)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki tsaftace naman ki ki masa yanka manya manya bakya buqatar qana nan yanka saiki juye shi a babbar tukunya (kina buqatar babban tukunya saboda dambun ki ya sake a ciki yadda zaki kyakykyawan suya) saiki kawo albasa dakika yanka kika gyara ki juye, tafarnuwa ki daddaka ki juye, curry sai kisa rabin robar, ki bar rabi, zaki juye thyme, maggi, citta, kanimfari ki hade su da naman ki gauraya kibar naman ki zuwa awa biyu saiki dora shi a wuta ki kawo ruwa daidai yadda zai shanye.

  2. 2

    Idan namanki yayi laushi zaiza kamar haka kina taba shi da muciya zai fashe, saiki tsaya ki sa muciya kina tuqashi

  3. 3

    Haka zakiy ta tuqashi har sai ya hade gaba daya

  4. 4

    Sai kisa mai da dan dama (man gyada ko na kanti)

  5. 5

    Zaki dauko Rabin curry dakika bari acan ki juye shi

  6. 6

    Saiki wanke taruhu ki jajjaga ki juye akai

  7. 7

    To anan zaki rage wuta sosai saboda zakiy su yan dambu baya son wuta a hankali ake soya shi saiki na tuqawa akai kai

  8. 8

    Kina tuqawa yana qara duhu shine alamar yana dauko soyuwa

  9. 9

    Gashi nan yadda kike gani a hoto ya qara yin jaaa(shi dambu yana buqatar jajircewa saboda yana daukan lokaci musamman in yanada yawa kamar wannan)

  10. 10

    Gashi nan kamar yadda kike gani man cikin dambun ya fara kumfa shine alamar dambun ki yakusa sauqa

  11. 11

    Fitowar mai kamar haka shike nuna dambun ki ya soyu ba sauran ruwa a jiki

  12. 12

    Gashinan

  13. 13

    Saiki tsame shi ki juye a cikin abin tacewa

  14. 14

    Zaki matsamin kina matse wa mai sai ya fita gaba daya

  15. 15

    Saiki baza shi ya huce sannan ki Adana shi yadda ya dace

  16. 16

    Done👍

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
rannar
Jigawa State Nigeria

sharhai

Aisha Adnan
Aisha Adnan @cook_27534734
me yasa dambuna baya laushi sai yayi kamar kayau kayau

Similar Recipes