Dalgona cookies

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Wannan biskit na yishi ranar farko da aka saka dokar hana fita a kano.Da farko nayi niyyar yin dalgona coffee ne wanda ake yayi a daidai lkcn,to gsky lokacin zuciyata bata kwanta da yinshi ba saboda ina tunanin zai yi daci,har na fara sai kuma na canza ra'ayina zuwa biskit saboda dama nayi kewarshi kwana biyu,nayi amfani da nescafe din da na buga ne da sauran butter cream da nayi amfani dashi kwana hudu kafin yin biskit din #FPPC

Dalgona cookies

Masu dafa abinci 4 suna shirin yin wannan

Wannan biskit na yishi ranar farko da aka saka dokar hana fita a kano.Da farko nayi niyyar yin dalgona coffee ne wanda ake yayi a daidai lkcn,to gsky lokacin zuciyata bata kwanta da yinshi ba saboda ina tunanin zai yi daci,har na fara sai kuma na canza ra'ayina zuwa biskit saboda dama nayi kewarshi kwana biyu,nayi amfani da nescafe din da na buga ne da sauran butter cream da nayi amfani dashi kwana hudu kafin yin biskit din #FPPC

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

40mintuna
4 yawan abinchi
  1. Kofi daya na butter
  2. Kofi daya na butter cream
  3. 1/8kofi na sukari
  4. Qwai daya
  5. Fulawa kofi daya da rabi
  6. Rabin cokali na flavour
  7. na kadadden nescafe Cokali Cokali 2
  8. Coakli daya na narkakken cakuleti Cokali

Umarnin dafa abinci

40mintuna
  1. 1

    Da farko a cikin kwano za a zuba butter zalla da sukari ayi amfani da whisker a buga har sai ya canza kala,a zuba butter cream a cakude,sai a fasa qwai a qara kadawa sai a zuba fulebo

  2. 2

    Sai a raba hadin butter din gida biyu a daya a zuba rabin fulawar da aka fada da farko a cakude shi ya hade jikinshi da kyau,a daya rabin kuma a zuba kadadden nescafe a cakuda a zuba narkakken cakuleti a qara cakudawa,sai a zuba sauran fulawar da yayi saura shima a cakudeshi ya hade jikinshi

  3. 3

    A ciro ko wanne daga cikin kwano a murzashi daban a saitasu su dawo dai daya,sai a dau daya a dorashi kan daya a nannade kamar tabarma a yayyanka a jera a farantin gashi a gasa.....naji dadin wannan biskit ni da ahalina nan take muka cinyeshi....🤣🤣daga baya dai na lalla6a kaina nayi dalgonan da na guda

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes