Lemon cucumber

karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
Kano

Wannan lemo ne wanda a koda yaushe ina yinsa sabida dadinsa da kuma amfaninsa a jiki sannan ga saukin yi.

Lemon cucumber

Masu dafa abinci 8 suna shirin yin wannan

Wannan lemo ne wanda a koda yaushe ina yinsa sabida dadinsa da kuma amfaninsa a jiki sannan ga saukin yi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

30mins
2 yawan abinchi
  1. Cucumber manya guda biyu
  2. Citta danya daidai gwargwado
  3. Ruwan lemon tsami cokali babba uku
  4. Sugar kwatan kofi

Umarnin dafa abinci

30mins
  1. 1

    Da farko zaki wanke cucumber din ki yanka kanana ki aje a gefe. Sai ki kankare bayan cittan ki yanka kanana.

  2. 2

    Zaki dakko blender din ki ki fara zuba ruwa Kofi biyu sai ki zuba cittar da cucumber din ki markada su sosai. Sai ki tace ki zuba sugar da ruwan lemon tsami. Zaki iya sawa a firinji yayi sanyi ko kuma ki sa kankara akai ko kuma kisha haka. Sannan zaki iya markadawa tareda sugar in kin tace sai ki zuba ruwan lemon tsami. Idan kin zuba a glasses din ki sai ki zuba grenadine syrup kadan shi zai sa kiga ya rabe ya koma kala biyu.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes