Gashin shinkafa mai lemo

A kullum Ana so adinga canza yanayin sarrafa Abu Ku kwada wannan dafuwa zakuji dadinsa sosai#team6dinner
Gashin shinkafa mai lemo
A kullum Ana so adinga canza yanayin sarrafa Abu Ku kwada wannan dafuwa zakuji dadinsa sosai#team6dinner
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara kazar ki,ki wanke ta.sai ki dauko robarki ki hade su madarar ki da duk hadin kayan Kazan nan a robar ki juya sai ki dauko kazar ki saka aciki ki juya ta sosai, ki saka a fridge yayi awa hudu
- 2
Sai ki daura ruwa kan wuta idan ya tafasa ki wanke shinkafarki tayi minti 10 ki sauke ki tashe. Idan ruwan duka ya tsane sai ki dauko tukunya ki zuba bota Dinki idan ya narke ki zuba shinkafarki tare da ganyen bay, magi 2
- 3
Asaka magi,tumatir na Leda cokali daya ko jar miya idan kina da shi, sai ki saka hodar lemo, sai ajuya sosai
- 4
Sai ki dauko abin gashi ki juye shinkafar
- 5
Ki dauko lemon zit ki yaryada
- 6
Sai ki dauko ruwan lemon zagi shima ki yaryada shi
- 7
Sai ki dauko kazar ki daga firij ki jera su
- 8
Ki yanka lemon tsaminki ki jerasu
- 9
Sai ki saka a abin gashi ki gasa.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


















sharhai