Dafaduka
Hmm dafaduka wato ina matukar sonta bana gajiya da cinta#team6dinner
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki wanke miyanki da su attarigu idan kina so zaki daka ko ki saka a gudansu, tafarnuwa ita ma zaki bare ki dakashi, ki bare maginki
- 2
Ki daura tukunyarki ki zuba mai tare da albasa ki soya, sai ki zuba su tamatir Dinki da kayan kamshi na rufe har sai da komai ya mutu sai na tsaida ruwa,
- 3
Da uwana ya tasafasa sai zuba shinkafata idan ta kusa dafuwa sai ki zuba soyayyen namanki
- 4
Sai ki rufe Ki jira ya dahu.kafin ya dahu sai ki dauko kwanki ki fasa ki zaka curry kadan, masoro,gishiri ki kada ki daura kasko kan wuta sai ki soya
- 5
Shikenan kin gama,sai dauko shinkafar ki zuba a kwano ki danna ki saka akan alamar kai sai ki sake zubawa acikin kwanon yadda kikayi ma farko haka zakiyi ki saka a kuwa da shi alamar ciki, sai Dan debo kadan kiyi kafa da hannu shikenan sai shinfida soyayyen kwanki akai,ki gutsoro kwan kadan kiyi ido.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes













sharhai