Miyar kuka mai naman kaza

Wannan miya, miyace ta gargajiya wadda akayita a zamanance don a kawata ta, ana cinta da tuwo ko wane irine
Miyar kuka mai naman kaza
Wannan miya, miyace ta gargajiya wadda akayita a zamanance don a kawata ta, ana cinta da tuwo ko wane irine
Umarnin dafa abinci
- 1
Za a dafa tsokar kaza da albasa da gishiri kadan tayi laushi, Sai a yayyagata sirara a ajiye a gefe
- 2
Sai a zuba ruwan dafa kazar a tukunya a zuba jajjagaggen tattasai da attaruhu da albasa adora a wuta
- 3
A daka daddawa tare da citta kadan da masoro da gyadar miya, itama a zuba tare da Maggi da dan gishiri a barsu suyita dahuwa har tsawon mintuna 15
- 4
Sai a kawo dagargajajjen tsokar kaza a zuba a Kara rufe ya cigaba da dahuwa na tsawon mintuna 15
- 5
Sai a kawo garin kuka, a rika zubawa kadan kadan ana kadawa da abin kada miya har yayi kauri
Keywords
Similar Recipes
More Recipes








sharhai