Yadda zakiyi hadin awara Mai sauki👌

Ina yima yarana hadinnan saboda suna sonshi sosai.
Yadda zakiyi hadin awara Mai sauki👌
Ina yima yarana hadinnan saboda suna sonshi sosai.
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko kisamu danyan awararki ki yanka ta dede yadda kikeso
- 2
Sannan ki daura mai a wuta danyi zafi sai kixu awararki da kika yanka ki soyasa,har yakare.
- 3
Sannan ki yanka albasarki Kar yayi girma sosai yankan sauce zakiyi Mata. Sanna kisata a maiyi kidan Bata tsoro👌idan ya fara laushi saki kisa dukka kayan Dan Danon harda curry kinuyasu su hade sai kisa ruwa Kan kibar albasarki ta silalu.
- 4
Da zaran ta silalu sai kidauko soyayyiyar awaranki ki juye akan albasar ki gauraya
- 5
Sannan kisuba attarhun ki.amma ni nayi amfani da yashi kadan sbd yara basason yayi zafi sosai.
- 6
In kikasa attarhun ko yashi sai kijiyasu in ruwan ya shanye sai ki Kara kadan ki barsa har awaranki ya turaru sannan ki sauke. Zaki iya samasa kayan lambu in kinaso.
- 7
Toh awararki ta kammala,aci dadi lafiya 😉🤤.da Haka nakawo karshen recipe Dina na yau sai mu hadu daku awani recipe din nagode 🙏 taku a koyawshe malaika's tasty bites ❤️🥰.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes









sharhai (6)