Shinkafa da wake
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko na wanke tukunya biyu babba da karami
- 2
Nakunna wuta na daurasu na zuba ruwa nabarshi ya tafasa kafinnan natsince wake na nawanke nazuba a karamin tukunya nadan sa kanwa dan yayi saurin dahuwa
- 3
Na debo shinkafa na nawanke kafinnan dayan tukunyan ya tafasa na zuba shinkafa ba na dansa Gishiri kadan nabarshi yayi parboiling
- 4
Naduba wakena naga nafara nuna sena juyeshi a colender nabarshi
- 5
Shinkafa ma daya fara nuna na tace shi na daurayi tukunyan namaida a wuta nasa ruwa kadan yadda zai karasa nunar dashi
- 6
Nakawo shinkafa da waken nahadasu waje daya na juya suka hadu nabarshi su karasa nuna
- 7
Nakawo mai nayanka albasa na soya na ajiye gefe nadauko guntun albasan nayanka kanana
- 8
Nakwashe shinkafa da wake na nayi serving nasa mai da maggi da yaji na se albasa shkn aci dadi lfy
Keywords
Similar Recipes
More Recipes






sharhai (3)