Milk-Butter cin cin(hausa version)

Nayi cin cin na butter yai min dadi sosai har na bawa wata kawata tana sana'ar, sai yanzu na hada da madara sai naji har yafi wancan dadi.
Milk-Butter cin cin(hausa version)
Nayi cin cin na butter yai min dadi sosai har na bawa wata kawata tana sana'ar, sai yanzu na hada da madara sai naji har yafi wancan dadi.
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki hade dukkan kayan hadin a roba amma ban da fulawa,
- 2
Zaki juya da ludayi sai daga baya ki zuba fulawar kadan kadan, ki saka hannayenki ki murza sosai komai ya hade.
- 3
Zaki gutsira ki mulmula ki saka wuka ki yanka.
- 4
Zaki rage wuta kamar na minti biyar dan cikin cin cin din ya soyu sai kuma ki kara wutar, ba'a juya shi dan haka zaki zuba mai ya shanye saman sa,
- 5
Da zarar yayi golden brown sai ki kwashe.
- 6
Zaki samu tukunya babba, ki zuba mai yai zafi sai ki jera cin cin dinki, ki lura kada wani ya hau kan wani(shi yasa zakiyi amfani da babbar tukunya).
- 7
Zaki tsane a colander yasha isa.
- 8
Dadi ba'a magana.
- 9
Similar Recipes
More Recipes











sharhai (3)