Farfesun kifi
Inason farfesun kifi sosai musamman catfish
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki gyara kifinki ki wankeshi da veniger kisashi a kwando ki rufe
- 2
Saiki gyara tattasai, Tarugu da albasa kisa tafarnuwa ki jajjagasu sannan ki karkare danyar citta ki gogeta
- 3
Saiki aza tukunyarki bisa wuta saikisa ruwa dai-fai yadda kikeson romuwarki saiki zuba daddawa da jajjagenki cikin ruwan,sannan ki saka maggi da gishiri kadan sannan ki rufe ki barshi ya tafasa kamar mintina 15
- 4
Sannan ki zuba kifinda Kika riga Kika gyara ki motsa da kyau sannan ki rufe.zakibarshi kamar 15-20mins sannan ki sauke
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11450779




sharhai