Indomie

Hmmm,ba irin dahuwar da muka saba yiba minti kadan an tafasa indomie,uwar gida,amarya,emmata a gwada wannan
Indomie
Hmmm,ba irin dahuwar da muka saba yiba minti kadan an tafasa indomie,uwar gida,amarya,emmata a gwada wannan
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki samu tukunya ki zuba ruwa ki dora a wuta har se ya tafasa,se ki zuba indomie dinki a ciki ki juya ta kaman minti biyu se ki tace ta ki rufe.
- 2
Se ki kawo agadar ki,ki bareta ki yanka se ki soya,ki kawo kwai shima ki soya.
- 3
Se ki kawo karas,koren tattasai da albasa ki yankasu da tsayi,se ki jajjaga ataruhun ki,se ki kawo kasko ki zuba mai ba da yawa b idan ya danyi zafi se ki zuba ataruhun ki a ciki,se ki zuba ruwa shima daidai,se ki kawo karas,albasa da tattasai ki zuba a ciki ki juya se ki rufe su dan risina.
- 4
Bayan kaman minti biyar se ki bude ki kawo maggi star ki zuba a ciki,ki kawo siga dan kadan ki barbada a ciki,ki kawo indomie din da kika tafasa ki zuba a ciki ki saka maggin cikin ta ki sa curry ki juya se ki rage wuta,ya zamana kadan take ci.
- 5
Bayan minti biyu zuwa uku se ki kashe wutar ki indomie dinki ta dahu, se ki zuba a plate ki kawo kwai da plantain dinki ki zuba a gefe ki kwashi dadi.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes






sharhai