Miyar tumatur Mai cabbage da caras

Safiyya Yusuf @samgz2703
Miyar tumatur Mai cabbage da caras
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki wanke kayan miyanki ki niqa kada yayi laushi sosai
- 2
Saiki dauko cabbage da caras Suma ki gyara ki yanka su day Dan girma
- 3
Sannan ki aza tukunyarki a wuta ki zuba Mai sannan ki zuba niqaqqun kayan miyanki ki rufe
- 4
Zaki barshi har ruwan su tsotse sannan ki barsu su soyu
- 5
Bayan sun soyu saiki zuba Maggi, gishiri da Curry ki motsa da kyau sannan kisa ruwa kadan,sannan ki zuba yakkakun cabbage da caras sannan ki rufe na kamar minti 7-10 sannan ki sauke
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11780467



sharhai