Alalan gwangwani da sauce din kabeji
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki surfa wake ki wanke ki fidda dusar sai ki gyara su tattasai,taruhu da albasa ki yanka ki zuba kan waken ki bayar a markado miki bayan an kawo sai ki bugashi sosai ki zuba ruwan dumi,manja,maggi da gishiri ki jujjuya sai ki kawo gwangwanin madarar ki wadda aka fafe kk wanke su da ruwan zafi
- 2
Ki shafa manja a jiki sai ki jera a tukunya wadda kk daura a wuta da ruwa daidai misali a ciki ki kawo tsaftattacen buhunki ki rufe sai ki rufa murfin tukunyar ki bata mintina ta dahu.
- 3
Sauce din ki farko zaki yi greating attaruhu sai ki yanka albasa,kabeji da tafarnuwa a wuri daban-daban sai ki daura frying pan a wuta ki zuba mai ki fara zuba tafarnuwa ki Dan jujjuya sai ki zuba albasa in tai kamar minti biyu sai ki zuba kabeji ki ta juyawa sai ki zuba su kori da maggi kina juyawa har sun yi laushi sai a sauke aci da alalan,😋
Similar Recipes
More Recipes



sharhai