Vegetable chips
Yana da dadi sosai,abun se wanda yaci
Umarnin dafa abinci
- 1
Wa’en nan sune abubuwan da ake bukata,zaki samu karas dinki ki zuba masa ruwan zafi ki barbada gishiri se ki dan tafasa shi kadan saboda ye laushi.
- 2
Se ki kawo kasko ki zuba mai a ciki dan kadan,se ki kawo tattasai ki zuba a ciki,ki dan kawo ruwa kadan ki zuba ki barbada gishiri da sugar ki juya se kisa murfi ki rufe kamar minti biyu.
- 3
Bayan kin bude se ki zuba albasa da karas dinki ki juya se ki sake rufeshi na minti daya.
- 4
Se ki zuba magin ki da curry se ki juya,se ki fasa kwai guda daya a ciki se ki juya.
- 5
Se ki kawo soyayyen dankalin ki shima ki zuba a ciki ki juya se ki rufe n na sakan talatin kawai se sauke ki zuba a faranti ki kwashi dadi.
- 6
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/12352377



















sharhai