Tandoori chicken toffees
Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan hadin dough din mu da na kaza, Da farko zamu yiwa Kazan Hadi mu tsumata.ki yayyanka kazar into cubes madaidai ta seh ki Sami roba meh fadi ki zuba,ki zuba gishiri-, chilli powder, corriander,garam masala,paprika-,cumin,fenugreek leaves,turmeric,yoghurt,ginger garlic paste,ruwan lemun tsami da dandano seh ki juya sosai koina ya Samu.
- 2
Ki rufe da Kling film ki sa a fridge tsawon hour 1 ya tsumu.bayan hour daya seh ki zuba Mai chokali 2 a frying pan
- 3
Seh ki zuba kazar a cikin Mai. Ki barshi ya dahu kinayi kina juyawa,idan ruwan jikin shi ya fito seh ki rufe ki rage wutar har ruwan jikin shi ya shanye kazar ta nuna tayi laushi.
- 4
Seh ki juye a faranti ki barshi ya huce.sannan ki kwaba hadin dough dinki.Ki Sami roba ki zuba flawa,gishiri,da Mai ki juya sosai ya hade,seh ki rika zuba ruwa kadan kadan kina juyawa har ya hade.seh kiyi kneading dough din ya hade jikinsa, kar dough din yayi ruwa Ana sonshi da Dan tauri.
- 5
Seh ki rufe ki barshi yayi resting tsawon minti 20 ko 30.Bayan yayi resting seh ki raba dough din gida biyu,seh ki dauki daya ki fadada da hannunki ki barbada flawa- seh ki Sami rolling pin kiyi rolling dinshi da fadi.
- 6
Bayan kin fadada shi seh ki Sami round cutter ko kofi ki fitar da round shape.seh ki dauki kaza guda daya ki saka a tsakiya,
- 7
Seh ki nade Kamar alawa kiyi twisting gefen seh ki sa fork ki fitar da shape din gefen,haka zakiyi har ki Gama,seh kiyi freezing a freezer na minti 15 kafin ki soya saboda ya Dan kame jikinsa.
- 8
Seh ki Dora Mai a kan wuta Amma wutar madaidai ciya seh ki soya kina Yi kina juyawa har yayi ja.Kina iya aje shi a zip lock bag a freezer har tsawon sati 3.Aci lafiya.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes


























sharhai