Miyar Ogbono

Inason sarrafa abinci kala kala musammman bangaren yarabawa,inason nauoin abincinsu 🥰😋kudai kawai ku gwada wannan miyar💯
Miyar Ogbono
Inason sarrafa abinci kala kala musammman bangaren yarabawa,inason nauoin abincinsu 🥰😋kudai kawai ku gwada wannan miyar💯
Umarnin dafa abinci
- 1
Nan ga abubuwan da muke bukata
- 2
Da farko zaki wanke kayan ciki ki sa a tukunya ki hada na namanki ki zuba maggi sa spices masu dadi ki tafasa har tsawon minti ashirin
- 3
Sai samu wata tukunyar ki zuba ruwan naman da ruwa kadan dai dai yawan miyarki saiki zuba nama da ganda da Kayan ciki da stock fish ki dafa minti sha biyar
- 4
Bayan ya dahu saiki zuba jajjgen attaruhu da albasa kisa daddawa ki juya sosai
- 5
Kisa maggi da gishiri ki juya saiki samu roba karami ki hada manja da ogbono ki juya
- 6
Saiki zuba aciki ki juya ki rage wutar ki barshi ya dahu minti ashirin amma ki dinga yi kina juyawa karya kone zakiga yayi yauki sosai.saiki zuba smoke fish dinki
- 7
Ki juya saiki kawo ganyenki ki zuba ki juya ki rufe bayan minti goma saiki sauke
- 8
Zaki iya ci da tuwo,sakwara,amala,eba🥰😋😁
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

























sharhai (4)