Fruity Zobo

sadywise kitchen @cook_13560156
Abinda yasa yazama na musamman saboda kayan itatuwa da akasa sai yabamu qamshi na musamman, na hadawa baqina sunji dadi.
Fruity Zobo
Abinda yasa yazama na musamman saboda kayan itatuwa da akasa sai yabamu qamshi na musamman, na hadawa baqina sunji dadi.
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko na wanke zobo na na zuba ruwa 4cups nasa citta, na'ana'a bawon abarba da kaninfari a dafa, inya tafasa kayan sun shiga cikinshi sai a sauke a bashshi ya huce
- 2
A yanka kankana, abarba da cucumber kowanne a markadashi sai a tacesu guri 1 a tace zobon nan da ragowar ruwanmu 16cups a hadeshi da ruwan fruits dinnan asa sugar a juya sosai, inyayi sai asa a fridge ko asa qanqara.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/13170756



sharhai