Miyar ganyen oha

#WAZOBIACONTEST .wannan miyar asalinta ta mutanen east nijeria(imo,anambra da sauransu) sewannan miyar tayi dadi sosai musamman idan aka hada da tuwon seno.kuma ganyen yana da daci zai mayar ma Wanda ya rasa dandanon bakin sa.

Umarnin dafa abinci
- 1
Ga kayan bukata domin miyar
- 2
Da farko Zaki aza manja yayi zafi
- 3
Idan yayi Zafi sai ki kawo nikakkun kayan miya(tarugu,tattsaida albasa) ki sa a tukunya
- 4
Idan ya fara motsawa sai ki kawo bushashshen kifi da kika wanke da ruwan Zafi sai ki saka a ciki
- 5
Sai ki zuba dandano da kuma iru(daddawar yarbawa)
- 6
Bayan kin saka sai kidan bashi minti 2 sannan sai ki kawo dafaffiyar ganda da kuma kayan ciki da kika tafsa yayi laushi sosai ki zuba
- 7
Sai ki rufe tukunyar ki barta har sai miyar ta dahu komai ya hade sosai sannan daga karshe ki kawo ganyen oha da kika wanke kika yayyanka ki zuba a ciki
- 8
Sai ki bashi minti 2-3 sai ki juye a mazubi.shikenan miyarki ta kammala
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

sharhai (3)