Dambun Shinkafa
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za'a barza Shinkafa sannan a wanke ta abarta a gwa-gwa ta tsane.
- 2
Sannan a yayyanka kayan Miya,kayan lambu,a daka su maggi
- 3
Se a dauko barzazzen shinkafan da aka ajiye ya tsane,se a zuba Maggi da kayan Miya da kayn lambu duka a ciki,se a zuba a gwa-gwa.
- 4
Za'a zuba ruwa a tukunya su tafasa sannan a aza gwa-gwa sama wadda bazata fada ba se a zuba dambun a aza marfin tukunya a sama se a bashi en mintuna kamun ya dahu.
- 5
Za'a sa Mai da yaji idan ya dahu aci dashi ko Kuma source😋
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/14700996









sharhai