Jollof din shinkafa me kayan lambu

Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
#sadakanRamadan #ramadan sadaka#iftar #sahur
Jollof din shinkafa me kayan lambu
#sadakanRamadan #ramadan sadaka#iftar #sahur
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki wanke shinkafarki da gishiri rabin cokali sai ki aza tukunya da ruwa ki bari su tafasa
- 2
In sun tafasa ki sa shinkafar da sauran gishirin tareda curry ki rufe
- 3
Sai ki yanka albasar da tarugu ki bare tafarnuwar duka ki wanke.
- 4
Sai ki dan jajjaga tafarnuwar ki samu tukunya ki zuba mai,targu albasa da tafarnuwa ki dan soya in kin soya ki saka ruwan nama da dandano da ajino moto sannan da kayan yaji.
- 5
Se ki tace shinkafar ki jira ta huce,in ta huce daidai lokacin ruwan sun tafasa se ki sa shinkafar in takusa yi kisa karas,green peas, masarar gwangani ki rufe.
- 6
In tayi ki sa a plate ki hada da naman kazar.Hmmmm ta yi dadi
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/14971776







sharhai (5)