Soyayyen dankali da kwai
Umarnin dafa abinci
- 1
Ki fere dankali ki yanka shi tsaye ki wanke ki tsane
- 2
Ki dora mai a pan idan yayi zafi ki zuba dankalinki kina juyawa har ya soyu
- 3
Ki fasa kwai a mazubi me kyau ki yanka albasa ki zuba jajjagen tarugu da tattasai ki sa dandano kiyi whisking
- 4
Ki zuba mai a pan kadan se ki zuba kwai
- 5
Idan ya fara soyuwa se ki dagargaza shi ki juya ko ina har se ya soyu
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16318970




sharhai