Dambun shinkafa da stew

Nayi wannan girkin ne a matsayin abin rana. iyalina sunji dadin shi mussanman ma oga 😋
Dambun shinkafa da stew
Nayi wannan girkin ne a matsayin abin rana. iyalina sunji dadin shi mussanman ma oga 😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na dauko tasanta tacem tukunya na zuba ruwa na daura a wuta na rufe saboda ya tafasa.
- 2
Kafin ruwa ya tafa na debi shikafa ta na gyara sannan na barza da blender na kuma tankade na cire tsakin.
- 3
Gashinan na fitarda garin da kuma tsaki
- 4
Na bude tunkuyar na samu ruwan ya tafasa sai na daura gwagwa akan tukunyar, sannan na wanke shinkafar da na barza na zuba a cikin gwagwar na rufe saboda ya turara.
- 5
Bayan kusan dik minti biyar ina dubawa in kuma juiya
daga nan sai na zuba curry, spices da kuma farin magi kadan da gishiri - 6
Na koma rufewa na tsawon minti biyar sannan na zuba cabbage da albasa wanda na riga na yanke na barshi ya isuwa sulala kadan
- 7
Bayan wadu mintina kuma sai na sauke nadan zuba mai
shikenan yayi - 8
Miya
Na tsaftace nama na tafasa shi kadan - 9
Bayan ya tafasa na juiye a wani wuri na zuba mai nasa albasa ya fara soyuwa sai na zuba naman na soyashi sama sama
- 10
Bayan ya fara soyuwa sai ba dauko nikakken kayan miya na zubasu a ciki saboda suma in dan soya su sama sama
- 11
Bayan sun dan fara soyuwa sai na zuba ruwan da na tafasa nama dashi nayi sanwa
- 12
Bayan nayi sanwa sai na zuba magi da curry da spices da kuma albasa
- 13
Na barshi ya nuna na tsawon 30minute. sannan na sauke
- 14
Sai kuma na zuba ma oga yaui testing
Keywords
Similar Recipes
More Recipes































sharhai