Tuwon dalayi

Tuwone Mai dadi ga santsi a Ido Kuma kamar sakwara next time zansa muku step by step pictures inkuna bukata
Tuwon dalayi
Tuwone Mai dadi ga santsi a Ido Kuma kamar sakwara next time zansa muku step by step pictures inkuna bukata
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko Zaki wanke shinkafa ki jikata da dare ta kwana
- 2
Saiki bada a markado maki ita kamar markaden kunu ko waina, idan Kuma da blender zakiyi duk dayane kawai dai na inji yafi laushi da auki
- 3
Idan an markado saikisa abun tata ki tace ko rariya Mai laushi nidai nayi amfani da abun tace Koko
- 4
Idan kin gama tacewa saiki zubashi a tukunya shi gasarar da kika tace din saiki Dora a wuta kisa muciya kiyita juyawa harsai yayi kauri note!
- 5
(Shi wannan tuwo ba'a barinsa idan an Dora a wuta kina dorawa kisa muciya kiyita juyawa harsai yayi kauri sanann imba hakaba zaiyi kullutai) idan yayi kauri saiki zuba Manshanu soyayye hmmmmm zakiji wani irin kamshi na tashi.
- 6
Saikisa leda ki kwashe note!(Idan an sauke kibarshi yadansha iska kafin ki zuba aleda imba hakaba ledar zatayi ta konewa ne Tanayagewa).
- 7
Zakiga yadanyi ruwayadanfi tuwon semo ruwa to ahaka Zaki sauke saboda idan ya huce yana Kara tauri, idan kin barshi da Dan ruwansa kinga zaiyi daidai kenan,
- 8
Kuma dadi kamar mu tsinke hannunmu, akwai yanda ake Banga soup a page din nan nawa idan Zaki gwada saiki duba.
- 9
Shikenan kingama ruwan dalayi anacinsa da miyar yauki nidai nawa da Banga soup naci sa
- 10
- 11
- 12
Keywords
Similar Recipes
More Recipes














sharhai (6)