Soyayyar doya da kwai

Nayi wannan girkinne saboda buda baki na azumin alhamis kuma ya kayatar dani 😋
Soyayyar doya da kwai
Nayi wannan girkinne saboda buda baki na azumin alhamis kuma ya kayatar dani 😋
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko na dauko doyata na ajiye gefe
- 2
Sannan na dibi daidai wanda zanyi amfani dashi na yanka yanda nake bukata
- 3
Bayan na gama yankewa na wanke na daura ta akan wuta nasa sugar da gishiri
- 4
Sai kuma na barshi ya tafasa sannan na sauke na tsiyaye ruwa na barshi yasha iska kafin in fara soyawa
- 5
Sannan na dauko roba na dauko kwai na fasa aciki
- 6
Bayan na fasa kwai sai na zuba jajjage na cikin kwain
- 7
Sannan na zuba magi da gishiri
- 8
Sannan na zuba flour da albasa
- 9
Sannan na kade kwai komai ya hade wuri daya
- 10
Sannan na daura mai a wuta yayi zafi na fara zuba doyar da na riga nasa cikin kwai
- 11
Bayan ya soyo sai na kwashe
- 12
Daga karshe nayi decoration da soyayyen nama
Keywords
Similar Recipes
More Recipes

















sharhai (4)