Shinkafa da miyar jajjage

Baby hadejia @cook_17645406
Shinkafa da miyar jajjage
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki fara dora ruwan dahuwar shinkafarki idan ya tafasa zaki wanke shinkafa kisa aciki sai kidan juyata kirufe ta dahu, idan takusa nuna zakisa taliyarki sukarasa tare, intayi zaki taceta sai kimaidata wuta ta turara
- 2
Zaki gyara kayan miyarki kiwanke ki jajjaga sai ki dora a wuta zaki dafashi har sai dan ruwan kayan miyar ya kone sai kisa mai ki soya bayan ta soyu sai kisa soyayyan namanki aciki tare da maggi d gishiri kicigaba da soyawa, sai kisa spices akarshe shikenan
- 3
Zaki wanke salad dinki sai ki yankashi kisake wankeshi da gishiri sai kibarshi ya tsane, sannan ki fere gurjinki ki wankeshi sai kiyanka tareda timatir da albasa
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16641804






sharhai (2)