Fatan doya Mai ganyan parsley da yanciki

Wannan fa irin karinsafen nan ga shayi kafkafra😂
Fatan doya Mai ganyan parsley da yanciki
Wannan fa irin karinsafen nan ga shayi kafkafra😂
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko Zaki tanadi duk kayan da nalussafa kaman haka nayankawa ki yanka
- 2
Sai kisa buttar ki nakaza ko Mai atukunya sannanki kunna wuta idan yayi zafi kisa cefane kisoya nawasu mintoci
- 3
Sannan kisa ruwa daidai yadda kike bukata kisa maggi gishiri,sannan ki dako doyanki Wanda kikafere kikayanka kika ajiye aruwa kisa
- 4
Sannan kisa curry thyme kijuya sannan ki kawo soyayyon yanciki Wanda kika gyara kika zafka kika soya sama sama
- 5
Kizuba ki rufe kibashi minty Ashirin yadahu sosai
- 6
Sannan ki kawo ganyan parsley Wanda kika kiki gyara kika wanke kika yanka kizuba dashi da Albasa ki zujuya kirufe na Yan mintonci baysn kin rage wutar sai ki sauke kizuba amazubi
- 7
Allah ya amintar da hannayenmu Aci lafiya nagode
Keywords
Similar Recipes
More Recipes





sharhai