Miyar wake mai kifi

Zainab Salisu @ZEENASS
Yara na suna matukar son miyar wake mai kifi,musamman idan na hada masu da farar shinkafa.
Miyar wake mai kifi
Yara na suna matukar son miyar wake mai kifi,musamman idan na hada masu da farar shinkafa.
Umarnin dafa abinci
- 1
Na gyara wake na,sai na wanke na zuba a ruwa na barshi ya dahu
- 2
Gefe kuma nayi jajjage tattasai da tumatir.Sai na yanka albasa ta na ajiye a gefe 1.
- 3
Sannan na wanke kifi na tafasa shi da albasa,lawashi,citta da garlic.kina iya sakashi a dayan ko ki murje shi.
- 4
Sai na dora pot na zuba mai da albasa na barshi ya fara soyuwa,sai na zuba jajjage na soya su,na zuba sinadarin danndano da kayan kanshi na barshi suka hada kansu,sai na zuba wake,kifi da ragowar albasa ta.Abarsu sudan kara dahuwa na 5mnts
- 5
Alhamdulillah, miya ta kammala,mun cita da farar shinkafa
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16810649








sharhai