Dafa dukan shinkafa da wake🍽

Dafa dukan shinkafa da wake🍽
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za’a dora ruwa a tukunya a rufe kafin ya tafasowa sai a tsince wake a cire duk wani datti da
Duwatsu sai zuba a zuba kanwa a rufe har sai ya kusa dahuwa sai a zuba shinkafa a gauraya idan ta fara dahuwa sai a tsane a kolanda a zuba ruwa a dauraye asa a gefe. - 2
Sai a maida tukunya kan wuta a zuba markaden kayan miya dan daidai idan ruwan sa ya tsane sai zuba manja a soya Ana jujjuyawa idan ya soyu sai a zuba ruwa dan daidai yanda shinkafar zata karasa dafuwa ruwan ze Shanye. Sai asa gishiri, maggi da kayan dandano asa kifi ko nama tare da Jajjagen kayan miya. idan ya tafaso sai a zuba shinkafa da waken nan a gauraya.
- 3
Idan ya kusa dahuwa sai a zuba yankakken lawashi (ganyen Albasa) a rufe ya turara sai a kashe a zuba sai ci. Aci dadi lafiya 😋😋😋 za’a iya amfani da ruwan Kaza ko nama wajen dafa shinkafar.
- 4
Keywords
Similar Recipes
More Recipes















sharhai