Garau garau shinkafa da wake
Umarnin dafa abinci
- 1
Na gyara wakena na tsunceshi tas na wanke na zuba a tukunya na zuba ruwa na dora akan wuta bayan ya tafasa na saka b powder tspn da gishiri na rufe zuwq 30mnt na wanke shinkafata
- 2
Bayan na wanke ta na zubata aciki bayana wasu muntuna ta tafasa na wankesu fa boiling na qara zuba ruwa kadan a tukunyar yayi zafi nakawo maggi da gishiri na zuba sai na kawo wann shinkafa da wake nawa na zuba aciki na rufe ya turara na sauke.
- 3
Na kawo salad dina na gyarashu tas na yamka bayan na yanka na wankesa tas da ruwan kal da gishiri na wanke tumatir da albasa na da cucumber na yanka su suma.
- 4
Kazata kuma dama inada ita na dakkota a fridge na wanke banida isassn mai kawai na gasata da mai kadan a pan shikenn na zuba a faranti naci abinci nah
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16822451




sharhai