Fatan tsaki Na Rama
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko dai xa'a nika kayan miya
- 2
Sai a soya manja da albasa idan ya soyu Sai a saka kayan miyan a soya shi fa kayan kamshi
- 3
Sai a zuba ruwan sanwa asaka sinadaran girki(maggi)Sai a Dan daka gyadan miyan ta farfashe sai a fece a saka aciki dan yayi laushi
- 4
Sai a gyara Raman a yanka a kuma wanke tsakin a rege saboda kasa.
- 5
Idan ruwan sanwa ya tausa sai a zuba tsakin da aka wanke a barshi yayi yan mintuna.
- 6
A daka crayfish ko a sakashi a haka,sai a zuba Raman da aka yanka a juya sai a rufe abarshi ya nuna
- 7
To fate ya kammala sai ayi serving
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/10475513




sharhai