Umarnin dafa abinci
- 1
A wanke nama a zuba a gwagwa ya tsane ruwan jikinsa,sai a zuba maggi,curry, thyme,dakakken citta da tafarnuwa,a yamutsa a zuba a roba mai marfi a barshi minti talatin ko awa daya.
- 2
A yanka albasa da tattasai da fadi a ajiy.
- 3
A hada yajin tsire da mai a ajiye.
- 4
A zira nama a tsinke, a gasa a oven ko a abin gashin nama sai ya gasu. Anayi ana juya naman.
- 5
A cire naman daga tsinke,a zira nama-tattasai-nama-albasa-koren tattasai-albasa har a gama zirawa.
- 6
Ayi anfani da brush a shafa wannan hafin yajin da mai a jikin nama,a mayar a oven minti 5-10 a cire.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/11211485





sharhai