Faten dankalin hausa

Nafisa Idaya(Ummu Nazifs Kitchen) @nafisaidaya
Gaskiya nayi matukar jin dadin wannan girki domin inason dankalin hausa kullum soyata nake sai nace Zan gwada fatenta Kuma aka dace
Faten dankalin hausa
Gaskiya nayi matukar jin dadin wannan girki domin inason dankalin hausa kullum soyata nake sai nace Zan gwada fatenta Kuma aka dace
Umarnin dafa abinci
- 1
Dafarko zaki fere dankalin hausa saiki yankata kanana ki wanke ki ajiye
- 2
Ki samu blender ko turmi ki nika kayanmiya da albasa da tafarnuwa ki ajiye
- 3
Ki daura tukunya akan wuta kisaka mangyada saiki zuba nikakken kayanmiya ko soya idanya soyu ki zuba ruwa daidai saiki saka sinadaran girki ki rufe daya tafaso saiki saka dankalin kibarshi ya nuna shikenan
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/14360969

sharhai