Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki markada tattasai da attarugu da albasa da ginger da garlic. Sai ki daura tukunya awuta kiyanka albasa kisa mai kisoya sama sama, sai ki zuba kayan markaden ki da curry da thyme, kisoya su tare
- 2
Sai sun soyu. Sai ki zuba ruwa kadan. Ki yanka carrot da green beans ki zuba kisa maggi da nama. Daman kin dafa naman
- 3
Ki rufe ya dahu sai kayan lambun sun nuna ruwan kuma ya rage kadan, sai ki kawo kus kus din ki ki zuba, ki yanka Ganyen albasa ki zuba ki juya ya hade sosai.
- 4
Sanna ki sauke daga kan wuta. Kibada minti kadan sai ki yanka lettuce (salak) da danyan tomato da cucumber ki zuba kijuyata. Kalas
- 5
Akula dai kus kus baya buqatar ruwa sosai. Ruwa kadan ya wadatar. Kuma indai dafa dukan ta zakiyi tofa karki barta awuta. Dakin zuba kus kus dai to ki kashe wutar
Similar Recipes
More Recipes




sharhai