Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko zaki gyara kayan miyanki tumatur attarugu tattasai albasa ki ki markada
- 2
Sai a dorai a wuta dadai yanda akaga zai Isa was markaden a soya da albasa idan akwai nama a wanke a zuba acikin mai idan ya Dan fara soyuwa sai a zuba markaden
- 3
Sannan akawo abunda zai kashe wa miyan tsami asa kamar dai baking powder ko kanwa duk wanda akeda shi asa sai a zuba gishiri kadan a daka tafarnuwa a zuba shima kadan daidai yanda kikeso idan bakyaso ma karki sa ki zuba Curry dinki ki juya saiki rufe tukunyarki
- 4
Ki dinga dubawa idan kinga alamun ruwan ciki ya fara karewa saura kadan saiki saka magin ki ki juya dakyau kiyita juya sosai idan kinga ya gaurayu sosai saiki kidan bari sauran ruwan ya kare zakiga miyar tayi ta soyu tayi kyau a ido haka zalika a baki akwai dadi 😆😋😋
- 5
Za a iya cida shinkafa taliya Alala da sauran abubuwan da akeci da miyan stew ma ✨✨✨
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (5)