Dambun alabo

Dambun alabo, nayi shi ne dan yau na tashi ina kwadayin shi 😃 😊
Dambun alabo
Dambun alabo, nayi shi ne dan yau na tashi ina kwadayin shi 😃 😊
Umarnin dafa abinci
- 1
Da fari na tankade alabo (gurka)
- 2
Sai na saka ruwa kadan na fara mulmulawa, ina mulmulawa ina saka ruwa kadan kadan.
- 3
Bayan na gama mulmulawa sai na saka ruwa kadan a cikin tukunya.
- 4
Na samu wani kwano wanda ruwa bazai hauro ta sama ba dan hayakin ne xai turara mana kuma ya nunar dashi.
- 5
Sai na samu leda na rufe zaman kwanon kamar dai yadda yake a hoto.
- 6
Sai na saka wanda alabon dana mulmula.
- 7
Sai na sake saka leda a samanshi, dan na rufe.
- 8
Saina kunna gas na barshi ya turara ya nuna na tsawon mintuna 15.
- 9
Bayan ya nuna sai na sauke dambun alabona nayi masa hadi na saka qulquli, maggi, albasa, tattashe da mai na hada.
- 10
Shikenan dambun alabo nah yayi 😋 da dadi fa sosai uwar gida a kwada da dadi sosai sosai 😋 😋 😋
😃 asha ruwa lfy. - 11
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
















sharhai (2)