Miyar wake

ZeeBDeen @ZeeBDeen
Na dafa ne ma iyali na, kuma nayi amfani da zogala maimakon alayahu
#Mukomakitchen
Umarnin dafa abinci
- 1
Karko zaa gyara wake a wanke kamar na kosai, sai a Dora shi a wuta a zuba ruwa cup 4 a bar shi ya fara dahuwa
- 2
A gefe sai a jajjaga kayan miyan a soya su da manja
- 3
A gyara kifi ko nama a soya
- 4
To sai a zuba wannan kayan miya cikin tukunya wake, asa dandano da gishiri, idan nama ne zaa yi amfani dashi sai a zuba lokacin
- 5
Idan ya dahu sosai sai a zuba ganye,, idan kifi ne sai a saka lokacin a juya a kashe wutan
- 6
Shike nan sai ci,, zaa iya ci da tuwo ko shinkafa ko aci haka
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16293979




sharhai