Miyan Katse
Adamawa recipe
Special miyar kase for my husband
Umarnin dafa abinci
- 1
Zaki samu tunkuzar ki ki mulmulata ball ball yan madaidaita sannan ki dora tukunyarki a wuta hade da ruwa
- 2
Ki gyara busasshiyar yakuwarki sannan ki wanketa tass ki zuba cikin ruwan da kika dora su tafasa tsamin ya fito sosai
- 3
Sannan ki kawo wnn tunkuzar da kika mulmula ki zuba a tukunya sai ki rage wuta sannan in kinsa baza ki sa cokali ba har sai tunkuzar ta dahu, kuma shi wnn tsamin yakuwan shi zai taimaka wurin hana tunkuzar wargajewa.
- 4
Idan ta dahu zaki ga tunkuzar ta Kara girma kuma zaki ga zai dan tsage kadan
Daga nan zaki wanke wani tukunyarki ki dora nama da albasa da gishiri bayan ki tafasa namanki sai ki zuba mai kadan a ciki sannan ki kawo jajjagen kayan miya ki zuba ki soyasu tare sannan ki dauka ki juye cikin tunkuzarki da yake dahuwa da yakuwa daganan sai ki saka maggi gishiri da curry sannan ki rufe yaci gaba da tafasa har sai ya miki yadda kike so, sai ki sauke shikenan miyar kasenki ya dahu. - 5
Kina iya cinta da shinkafa ko tuwon shinkafa ko bredi
Note: Idan kinji yayi tsami kina iya saka mata kanwa kadan sanñan kina iya amfani da manja a maimakon mai ko kuma kifi a maimakon nama ko ki hada duka, sannan zaki iya sa ganyen albasa ko alaiyahu.
Keywords
Similar Recipes
More Recipes




sharhai (5)