Miyar gyada
#gyada mai sihiri, miyar gyada akwai dadi sosai
Umarnin dafa abinci
- 1
Farko zaa jajjaga kayan miya, sai asa mai kadan a tukunya a soya su
- 2
A dafa nama a soya shi a ajiye gefe
- 3
Sai a zuba ruwa kadan, a daka gyada a zuba a barshi yayi ta dahuwa, in ya dahu sosai sai a zuba dandano da kayan kamshi
- 4
In ya dahu zaa ga mai ya fara fitowa sai a gyara alayahu a zuba da nama sai a kashe wuta kar alayahu ya dafe
- 5
Sai a zuba aci,, ana iya ci da tuwo, biski, alkubus, fankasu ko couscous
Keywords
Similar Recipes
More Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/16479743





sharhai (6)